Monday, 6 February 2017

Zabina

💐💐ZABINA💐💐1&2 By miminnoor Zaune take cikin mota tana jiran yar uwarta, baba japaru Wanda yake direban su Mei kimanin shekara hamsin , yaxo Yana tambaya ameera wacce tagaji da jiran amra " Wai Ina amra ne ita kullum sei anjirata" hakan yayi deidei da fitowarta, riqe take da jakar makarantar da Sapa a hannu tayi sauri tashige mota inakwana baba japaru tafadi a hankali, ba tareda ya kula taba yaja mota suka fita....yasauke su a makarantar sannan yanupa ofishin oganshi Wanda yake mahaifinsu .Wacece ameera Kuma wacece amra amrat da ameera eya'ya ne ga alhaji ukasha lawaal mahaifiyar ameera( wace sunanta zainab) itace UWARGIDA. Amma Bata samu haihuwa da wuri ba sei ta shawarci mijinta da ya qara aure ko Allah zei Bata, Bayan hakane alh ukasha ya auro fateema mahaifiyar amra... Abun dake tsakanin amra da ameera watanni hudu ne kawai,(ameera ta girmi amrat da wata daya) hakan yasa ake kiransu da tagwaaye Amrat kyakyawace ajin qarshe. Sabida Allah yabata diri iya diri, nonuwarta acike suke gakuma hips masha Allah ita ba Para bace Kuma ba baka ba tanada ido Dan deidei, Hacinta Dan deidei ga Kuma yar qara Mar bakinta Kai kace teaspoon ce kadai ke shiga gakuma whushirya ga gaashi kamar India tabarkallah Itakuwa ameera Para ce sosai kamar mahaifiyar ta Kuma ba siririya bace Allah yabata dukiyar fulani itaba daguwa ba ita ba gajera ba tsawon su daya da amrat seidei ita amra tafita shape kowa da kyaw da Allah ya bashi Sanye suke cikin wani uniform Mei skirt sky blue da shirt pari sei Wes-coat light blue kalar skirt din... Uniform din ya anshesu sosai barinma amra wacce uniform din yakamata sosai yafito mata da shape dinta matuka hakan yasa mahaifinsu beison uniform din 💐💐ZABINA💐💐 3&4 by miminnoor Suna sauka a mota sukayi assembly hall da sauri, Garin sauri amra ta take wani batasani ba.tayi sauri tadago Kai tana qoqarin tabada haquri Amma sei ya hauta da masipa, ke wace kalar wawiya ce, ke mahaukaciyar inane, baki Ganine,banza qazama.... Jikake tassss... Amra ce ta wankeshi da Mari. Hakan ya jaayo hankalin dalibai da dama, riqe wajen yayi sosai yaji zaapin marin Amma yakasa komi cak ya tsaya Yana kallonta sabida tunda yake baa taba marin shi ba,,, muryar principal sukaji Yana what is happening over there.. Duk suka koma Kan laayi banda amra wacce Takoma Klass tayi kwanciyarta har aka qaare assembly duk suka Koma classes Ameera ce tayi Klass dasaurii tasami amra kwance... Buga Lockern ta takeyi da karfi tafara masipa " Amrat what was the meaning of what you did at d assembly hall, Kibani amsa" cikin hawaaye amrat ke magana "ke bakiji names din da ya Kira niba Wai qazaama wawiya fa habba, Nanko ameera ta shiga rarrashinta don ko kadan batason Ganin bacin ran yar uwarta balle ace hawaaye Can Kuma ss2b Faisal ne yake Bama abokinsa Anwar haquri Wanda shikuma yaki saurari sei masipa yake "who d hell dos she thinks she is, Dole NE nakoya mata lesson.... Ko tasan ni waaye... Shigowar physics teachern su ne yakatse maganar da suke.... Har aka tashi ranar Anwar Baya cikin nutsuwa 💐💐ZABINA💐💐5&6 by miminnoor Shagwaba take tana riqe jakar umman ameera.. Dan Allah umma babba zanbiku... Please sweet umma.. Umminta tajuyo tana mata masipa. Wai ke amrat yaushe zaki girma ne.. Ke kullum kamar yarinya... Umman ameera tayi dariya tace ki bar mun ita, tajaayo ta tarada mata Abu akunni nidai mimi banji ba gani nayi dei amrat na dariya.. Sei Kuma tayi upstairs aguje har suka saamu suka tafi, Tuni tamanta wani Abu yafaru a makaranta ... Dan ko chatting ta hau yi daka ganta kasan tana cikin nishaadi Anwar kuwa Yana kaiwa gida dakinshi ya nupa ya cire uniform Dan ko saashen su mom beije ba.... Yazo cire Sapa yaga shedar inda amrat ta takaashi , nanko komi yapara dawo masa daga Parko , cire sapan yayi ya wurgata qasa... Sei saqe saqe yake azuciya... Yashiga baaayi yayi wanka yayi alwala yayi sallah.. Sei ya pada Gado ko Tunanin Mei yake oho Naga yadanyi murmushi wanda ya bayyana masa dimple dinshi(jst lyk my noor).... Bacci kuwa yayi halinsa kuwa.. Haka yayi bacci abunsa Mom sei neman son dinta Takei atunaaninta bei dawo ba... Shiga Dakin shi tayi, tayi mamakin Ganin shi Kan gado Yana sharara baccinsa... Yayi kyaw Sosai don koni mimi yamun kyaw🙈 Wai shin waaye ne Anwar...? Asalin sunanshi OTHMAN BELLO AHMED... Mahaifinsa haiffafen Dan yola ne mahaifiyar shi kuwa hajiya salmat Salaam yar gombe ce.... Daka gansu kaga fulani seidei shi Anwar ba fari bane sabaanin iyayenshi Wanda suke farare kamar Yan India. Anwar haddaden namiji ne ajin qarshe danko ba gajere bane.... Slim guy ne Kuma wankan tarwada danko kwata kwata ba baqi bane...gaashin Kanshi baki ne sosai Kuma akwance take kamar na larabawa... Dimple dinshi Mei daukan hankali...Anwar daane tilo awajen iyayenshi Kuma beisan Yan uwan mahaifinshi ba.... Don alhaji ukhasha cemasa yayi duk ba a Nigeria suke ba. 💐💐ZABINA💐💐7&8 Yau Thursday.... Wanda yake ranar sport na ibzy Britain college....... Sun sha track suit da daurin dankwali fari wasu MA ko dankwalin babu... Mazan MA track suit suka Saka duk sun hadu. Gilin gilin gilin qarar babban agogon dake bangon makarantar akeji. Makaranta ne yaran manya... Musamman yayan Yan siyasa shiyasa suke abun da suke so batareda takura ba sei dei akwai discipline Amma baa duka😶...... Haphsert bako yarinya ce mai rawan Kai... Kuma ita a zuciyar ta Anwar take so... Hmm shiko gogan gani yake kamar duk yammatan Ibzy Britain college babu class dinshi.. Kai kaaji miskili......Don ko Anwar mutum ne Mei ji dakanshi. Kiran haphsert yayi wacce akafi Kira da chi chi... Taxo tana tafiyar rangwada, ya akayi Dan 'B' yayi murmushi wanda yafito masa da yar dimple dinshi... Yace akwai aikin da zaki munne.. Tayi dariya tace ai duk abunda kakeso zanyi tana magana tana zuge zip din jacket dinta tana pari da ido shiko Sam bei lura ba.... Matso da kunnen ki.... Yarada mata Abu akunne Wanda ni banji ba. Ajiyar zuciya tayi alamar task din zei mata wuya, Amma sei ya kwantar mata da hankali tare da CEWA " I PROMISE I WON'T IMPLICATE YOU" toh pha nidai mimi matar sadeeq sun saani aduhu Duk sun koma klasses after a very long period of sports, seiga discipline master su Wanda suke Kira da Mr cane Amma asalin sunanshi Augustin adaaju bayarabe ne Kuma acewan Yan makarantar azzalimi ne..... Yashiga ss1 Sci .... Duk suka miqe tsaye.. Yayi announcing Wai Ana nemar wata missing fone. Nanko aka shiga searching... Aiko sei ga waya a jakar amrat 😳Garin ya haka....... Hmmmm nanfa aka fara rikici.... Akatafi sei office din principal "Mr vishal Kumar" wani Dan India haka law yakaranta Amman Baya practicing..... Nanko aka shiga solving case har aka gaano inda matsalar take da taimakon nafeesat wacce taji zancen Anwar da hafsat ko ya akayi taji oho. Da aka Kira anwar bei Musa ba seidei yayi qoqarin rufawa hafsert asiri..... Acewanshi Bata ciki shine yayi aikin da kanshi. Hukuncin da principal(barrister kumar) ya yanke Akan anwar ba mei wahala bace.... Kawai special assembly zaayi masa Kuma zei Ba amrat haquri in public.... Hmmmm tashin hankali.

💐ZABINA💐10&11by miminnoor

Bangaren Anwar kuwa Yana kaiwa gida... Babban parlour ya shiga. Yarungumo mom Yana hawaaye... Duk hankalin mum ya tashi.. Don Bata taba Ganin son dinta a kalan wannan yanayi ba..... Babana ya akayi meyasameka... Kuka kawai yake kamar yaro danko abun da yafaru amakaranta na cimmai rai.... Nanko mum tashiga rarrashinshi har tasamu yayi shuru... Zama yayi aqasa ita tana Kan 2 seater.. Nan Anwar ya zayyana mata komi daga farko yanda ta mareshi ha inda akace ya Bata haquri...
Umma tayi mai fada sosai Kuma tamasa waazi duk wani laifi shi taba..... Tamasa nasiha sosai Kuma ya gamsu. Ya hau Sama yashiga daki ya cire uniform sei wanka yayi alwala... Yasha shadda Para hula baki takalminsa Dan palm slippers Mei tsada baki. Ya peshe jikinshi da turarika masu matukar qamshi.... Ya dauki daddumansa akafada... Zai tafi masjid.... Yayi kyaw matuka kamar asace😉.... Fitar shi keda wuya suka hade da babban abokinshi FAISAL..... Maxxa ashe gara da nazo da wuri da shiknn seidei nazo banganka ba kawani sha hula kamar ango faisal ya fada cikin tsokana... Kai kasan wannan muyi sauri Kar mu makara

Bayan an idar da sallahn.... Sun dawo gida Faisal yayi hanyar gidansu.... Anwar yayi room dinshi. Fada wa yayi Kan gado agajiye, Tunanin amrat ne Yazo masa.... Yayi nadamar abubuwan da yayi mata Kuma ya qudurta aranshi zei Bata haquri, ranar Monday.... Saanan yatuna ashe akwai jarabawa..ya dubi time table yafito da littafi zeiyi karatu Hmm (kaji serious student😂ba irinsu wae ba😜)

💐ZABINA💐by miminnoor

Bangaren amrat Kuma Bayan ta idar da sallar Isha'i.... Tayi addua ta kwanta.... Barcin ko yaqi zuwa sei juyi take Akan gado kamar waina. Takasa bacci Tunanin abunda yafaru a makaranta takeyi. Duk tabi ta damu gani take kamar ta cuci Anwar. Tanaata daura wa kanta laifi Sam bataso Amma Anwar haka ba. Tashiga wani halin rudu . Cikin wannan Tunanin take har Allah yasa bacci ya kwashe ta.

Sadeeq Musa ahmad... Wani kyakyawan saurayi ne Mei kimanin shekaru 21 a parlourn su amra..Dan uwansu amra ne ., mahaifinsu ameera Kebin mahaifinshi. Zaune yake Kan sofa...... Sanye yake cikin qananun Kaya. Umma tashigo.... Yayi sauri ya gaidata.. Ina kwana umma yawwa baffa antashi lfya alhmdulilah ya amsa mata Kanshi amasa. Ina ameeran...Bata fito bane... Yace eh Bata fito ba.... Umma tayi ciki tana qwala wa ameera Kira AMEERA AMEERA... Naam muryar ta tajiyo a Dakin amra. Tabude kofan Dakin... Mei kuke yi ne har ynxu.... Amra Dan Allah kibar fusk anta haka sei kace wata amarya umma tafada cikeda tsokana.... Dariya sukayi amra tace umma na nakusa gamawa.... Tace toh kuyi sauri Dan Allah Yana jiranki.... Ameera tace toh... Dasauri tasauko..... Sadeeq sake baki yayi Yana Ganin ikon Allah.... Yanda ameera tayi kyaw gashi make up dinda amrat tayi mata ya fito da kyawn ta sosai.... Sanye take cikin atampa red Mei wrapper skirt da bakin gyale takashe dauri...... Tahadu sosai.... Taku take cikin nutsuwa da kunya... Jikake qwas qwas qwas Karan takalmin ta Mei tsini..... Duk jikin sadeeq ya mutu Ganin yanda ta yi kyaw kamar sabuwar tawraria, Koni miminnoor seida nayaba.... Gaskiya amrat ta iya makeup dayake maabociyar kwalliya ce...( Nidai idan bestiee reemah zatayi aure wajen amrat zatazo makeup😉)
Kallon ta yake kamar ya hadiye... Qamshin turarenta daya bugi hancin shi ya parpado dashi daga maparkin dayake 😜
... Murmushi take kamar izzah taga nura 😂..... Yakike yace mata muryar shi qasa qasa... Tace lfya, ya gida, klau, sei Kuma shuru 🙄kowanne na Satan kallon juna.... Wai kunya🙃
Amra ce tashigo musu da coffe ☕ ND biscuits a tray.. Tawani zumbula hijabi... Dariya yashiga yimata Yana tsokanarta... Amratutu kece yau a hijabi. Dariya tayi tana Cewa kaga Yaya sadeeq banison kana mun haka fa ai dama Ina sawa, yayi murmushi yace toh nidai bantaba Ganinki dashi ba...

💐ZABINA💐 14& 15na miminnoor

Ynxu Yaya sadeeq sheidan da zakayi akaina kenan.um Kai dei kaji da wacce ke gabanka ni kadaina samun ido,, Bari zanje na ziga su Abba ayi ayi a daura muku aure muhuta kun daame mu... Kallon ta ameera tayi ta balla mata harara.  Itako dariya take harta bar musu parlourn.

Yau shine yake marking end of term examination din ibzy Britain college Wanda aka Hada duka dalibai ranging from ss1-ss3 a wani babban hall (examination hall).

Kowani seat Yana dauke na number haka Kowani student da number da aka bashi..... Duk sun natsu sun zauna Ana jiran afara Raba papers.... Ameera tana seat number 24 Anwar number 25 amrat number 10 Faisal number 55.

Anwar da ameera na kusa da juna... Haka suke rubuta jarabawarsu ko magana babu.... Da kayi magana ko da kadan ne tamkar baka rubuta papern ba.
Ynxu har sunyi kwana 3 dafara jarabawa Amma Anwar bei hadu da amra ba ..... Kullum Anwar kamar ya tambayi ameera Amma seiya kasa 😒gashi Yana so yaba amrat haquri.... Itama amrat tanason ganinshi Kuma tarasa dalili duk da tsoronsa takeyi. 
Wani abunda Anwar bei lura bane kalan kallon da ameera ke masa a kullum. Duk wani abunda Anwar keyi Akan idon ameera ne..... Don Koda sun zauna sei tayi qoqari Koda hanunshi ta taba🙄Kota Gama papernta sei Anwar ya tashi zei fita take fita. Komeyasa??

Ramatu tashigo cafterian tasamu ameera azaune ita kadai tasa hannu tayi tagumi... Tana zuwa tafara mata tsiya... Bestiee Tunanin Mei kike.
Ameera tadago Kai da sauri... Aminiya har kin fito... Rahmatu tace eh wllhy ynxu muka Rabu da Abba a library..... Toh masoya Allah yabarku tare.... Rahma tace ameen.
Ina Yayannaki rahmatu tafada cike da tsokana.... Tsaki ameera tayi tace ni Dai kabarni baashi yadameni ba.
Rahmatu tace eyyeh toh waya dameki ynxu....... Wllhy aminiya kamar na fara fadawa kwadon soyyayar Anwar fa 😟..... M really in luv with him....he's so cute adoring I don't know bestiee words can't explain...

WANNAN MISHKILIN DABAYA MA KOWA MATASA.......... Rahmatu tazaro ido..... Amee Ina zaki ijiye Yayannaki.. Kinsan bezei yiwu ba.... Tunda iyayenku sunsan da zancen ku

Murtuqe fuska amee tayi..... Ni Dan Allah kadaina maganar sadeeq. Ni ynxu kifada mun yanda zanyi handling gaayennan pls... Wllhy m nt my self... Har wet dreams inayi duk Akan anwar fa... Jex help me out kafin abun yafi qarfi

Ramsey ta tabe baki....  Sannan tayi  Ajiyar zuciya.... . Kinsan Anwar ne bei damuda mata ba..... Don ni tunda Nike Bantaba Ganin shida wata ba.. Banda wannan haphsert bakon data naace masa.... Amma karki damu.. Zamusan tayi

Yau ne Ranan exams taqarshe...... Kuma Friday Wanda kowani Klass paper daya garesu islamic religious studies. Ansamu delay daga wajen teachern da zei kawo paper hakan yaba dalibai Daman surutu...... Invigilators dake hall din suma surutunsu suke yi..........
. Banda Mr isma'il Wanda yake kula da harkokin dalibai maana student affairs. Ganin yanda su Anwar suke ta surutu (musu sukeyi Kan qwallo ) yasa Mr isma'il ya canza musu seat. Ya maida Faisal can gaba.... Anwar Kuma yamaida shi seat 11 kusa da amrat...wacce tasaka Kai Kan locker..... Bei lura itace kusada shi ba Itama batasan ancanza mata seat mate ba.

Can ko seiga exam papers sunzo both CRK ND I'm. Suka fara paper..... Pen ✒ din amrat ne yafadi taduqa zata dauka taga takalmin maza.. Itakam tasan seat mate dinta mecece.... Ahankali tadago tana Ganin Anwar ne taji gaban ta yafadi. Tsoro yabi ya mamiye ta... Allah yasa tagama papern dako rubutu bazata iya ba.... Shiko Anwar bei MA lura ba.... Question paper ta tadauka tajuya.. Sei ta rubuta " I AM SORRY" Amma Kuma takasa miqa masa badan invigilators ba sabida invigilators din ba Masu zaafi bane.... Sei dei kawai tsoro datakeji.... Daurewa tayi ta ijiye masa Kan locker... Yayi sauri yadauka kaman Mei jira.. Ya na dubawa yaga I am sorry seiya juya ya kalleta.... Abun mamaki sei yayi mata murmushi.... Hakan ya kwantar mata da hankali

Seiya juya paper ya rubuta "m sorry too" yamiqa mata takaranta ko ahaka ta kasa kallon fuskar shi

Tatashi tayi submitting answer sheet dinta sannan Anwar ya lura da kalar hallitar da Allah ya mata.... Yar gajerar flay skirt dinta da bei wuce gwiwa ba yayi mata kyaw Sosai... Binta yayi da ido har ta fita..

💐ZABINA💐16&17 by miminnoor

Ameera kwatakwata Bata Jin dadi don yau Bata zauna da Anwar ba ko ganinshi Bata yi... Gaashi rahmatu tahado mata turarika masu qamshi Mei jaayo hankalin mutum... Itakadai tazauna papern MA takasa rubuta komi. Haka aka tashi ranta abace

Shiko Anwar yafita da sauri kozeiga ga amrat... Amma Ina tariga da ta yi hanyar gida. Ameera kwatakwata Bata cikin farin ciki... Tazaba MA kanta zaman kadaici kullum tana daki rungume da pillow... Gabadaya tabi ta baci abincin MA Bata ciba.... Amrat tabi ta damu da haalin da yar uwarta tashiga... Kullun seita tambaye ta Koda matsala seidei tace batada lfya ne...yau ciwon ciki gobe ciwon Kai... Excuse dinta knn. Kullum.. Sadeeq MA idan Yazo Bata bashi. Hankalinta harnafara shiga damuwa....

Gashi ranan Monday zasu yi funday dinsu na makaranta... Ameera gandauki take zata ga AnwarI. Shiko Anwar tunda yakai gida yake farin ciki har Faisal ya lura dashi Amma yaki fada MA Faisal dalili. Tun ranar Friday yake tason Jin muryar amrat shidai kawai yanaso yasake Ganin ta.

Wasu tambayoyi ne kamasa yawo a kai.... "y do I want to see her", y m I always thinking about her, meyasa Nike son Ganin tafiyar ta"ANWAR wake up Kardei sonta kake.... No it can't be.

Ya zaayi kafara son yarinyan da ko sunanta baka sani ba.shi ke ki dinshi Kuma shi ke rawan... Ni miminnoor harnafara tsoro yanda naga Yana magana shikadai 😅

Qarfe 8:00am suka tashi har ummi tafara masipa "bazaku je makaranta ba? Ace har ynxu Kuna kwance..... Ameera datake bathroom tana shower 🚿 tayi ta sauri... Tafito daga ita sei yar qaramar pink towel... Tabazo gashinta ajike.. Ummi tabude dakinta ke sei yanxu kikayi wanka ko bakuda skul ne... Ummi akwai Amma yau funday Kuma sei 9:00am zaa fara activities.... Bakayan garinku zaku sa ba? Ummi tafada tana kokarin rufe kofar Dakin... Amee tace a'a wannan cultural ne Kuma sei gobe.. Batareda ummi takulataba ta nufi hanyar Dakin amrat wacce tadade gaban morrow... Tana ma fuska ta makeover...
Ummi tashiga tazauna gefen gadon yarta... Wacce ta yi nisa a sa eye liner.... Seidata gama tace inakwana ummi na... Yawwa Cinderella antashi lfya...amrat tayi Daria tace alhmdulilah ummi na..

💐ZABINA💐 na miminnoor 18&19

Allah yamiki albarka tayi MA yarta addua sosai Kuma tamata nasiha sannan ta tashi zata fita... Sei amrat tace ummi ni bansan kalar kayan da zansa ba.... Ashagwabe take MA umminta shagwaba... Bari yar uwarki tashigo seitazaba Miki... I zanje nayi break fast..... Cikeda mamaki amrat tace breakfast Kuma kande Bata Nan ne?

Eh tatafi qauye.... Jikin mahaifinta ne ya tashi.... Oh toh Allah ya qara sauqi.... Ummi tace ameen... Kuyi maza kuzo kugaida umma batajin dadi Uhmm kawai amrat tace.... Har ameera ta Shirya amrat nagaban madubi..... Tamkar amarya tamaida kanta.... Ta yi parking gashinta da ribbon pink.... Tabarkallah masha Allah.. Sannan tafara shapa turarika ajiki qamshin humranta Mei dadi....Jin qamshin wani kalan turare Mei daukan hankali ne ya sa tajuya... Ganin ameera ce sei ta cigaba da shape shaapenta

Amma wannan wani turare ne amrat ta tambaya " murmushi ameera tayi tareda zama Kan shimpidadiyar gadon amrat.... Rahmatu ce ta hado mun6,meyasa kika tambaya..." bakomi Naga turaren akwai dadi.. Nima inaso"mutuqe fuska ameera tayi tace komi ni kedashi seiki ce kema kinaso, amrat ta marairece mata "toh Dan Allah kitsamun kadan ko na yau ne kawai please ta Yaya sadeeq... Hakan data fadi yaqara Bata haushi don ita kawai Yayan nata yafita mata Arai..... Haka ta daage tayi murmushin Dole tace toh idan kin Shirya sei kizo daaki na

Yawwa swt sis Amma fa bansan kayan da zansa ba.... Ameera tace kisa kowanne mana Kaya is Kaya... Amrat tamata wani kalan kallo"yoo dankinga kinyi kyaw shiknan nikuma nasa kowanne ko"

Ameera tayi kyaw Sosai... Tasaka wata atampa super red Mei ratsin Purple Kuma aikin jikin blouse dinma Purple yayi kyaw Sosai abunka da farin mutum

Wrapper skirt ce sei Kuma takalminta Mei tsini Purple da yar karamar gyale Purple sei jakar zamani Itama Purple.. Taci Dan simple make up, powder sei Jan baki da Dan kwalli....

Ta kashe daurinta Dan ko ameera gwana ce wajen dauri gashinta da tayi rolling ya bayyana atsakiyar daurin.

Nan akashiga neman MA ameera kayan da zata sa... Parko tasaka jallabiya takuma cirewa tasaka wani English gown Itama ta hadu Amma still ta cire duk tabi ta hargitsa Dakin sabida ruwan ido😂

Dagyar a kasamo daya... Wata gown ce wacce takamata daga Sama daga wajen waist dinta har qasa asake take hakan yabada A shape shadda  torques blue taji aikin pink daganin aikin kasan Mei tsada ce.....yayi mata kyaw Sosai bakadan ba don yafitar ea shape dinta kam
Ameera ce ta kashe mata dauri kalanna amare gashinta ta datayi masa nadi ya bayyana atsakiyar daurin..... Tasaka takalmi yar flat slippers pink da yar qaramar gyale pink sei jakar ta na zamani Mei chain hand torques blue

Tayi kyaw fiye da tunani danko ameera seida tayi kishin kyawn ta..... Kamar waya amarya duk sinsha zaanen dyes ahannu.. Na ameera yafi haskowa dake parace sosai

Suna sauka suka shiga mota.... Baba japaru ya Kai Abba airport Dan haka su suka Kai kansu makarantar ko breakfast basu tsaya yi ba acewar su sunyi latti... Ameera ce kejan mota wata yar karamar KIA ce.

💐ZABINA💐 20&21 na miminnoor

Bangaren Anwar ko shi har ya Manta akwai wani funday... Yana daki sei sharara baccinsa yake hankali kwance

Faisal ne ya shiga dakinsa yaganshi Yana barci..... Salaati yashiga yi Wanda muryasa yatashi Anwar.... Kallon agogo yayi Shima yasaki innalilahi... Haka lokaci yaqure sorry 🙏 Faisal wllhy sei Bayan subhi nasamu barci..... Barinayi sauri na kintsa shiko Faisal binsa yayi da kallo

Cikin Yan mintuna Anwar yafito da towel a kwankwanso dayan Kuma akai Yana goge ruwan Kanshi.... Faisal Wanda yashagala da danne dannen waya bei MA lura yafito ba...

Yashapa mai ya peshe jikin shi da body spray saanan ya Bude drawer sa yafito da wani shadda light blue Mei gajeren hannu Kuma rigar Bata Kai gwiwashi ba rigar ta kame siririyar jikinshi sei wandon dinkin zamani🙂

Sei baqin hula dasaka Wanda yaqara bayyana Masa kyawn sa.... Kwantaciyar baqin gashin Kanshi Mei qyalli Wanda ya hade da sajaen fuskar shi yakara sa shi kyaw.... Yasa takalmi baki ya pesa turarika masu dadi
Oya muje.... Kawani zauna kamar bakaine kake ta rapta sauri ba daka shigo..... Faisal yatsaya Yana kallon shi yace wow..... Yanaga yau kayi dabanne harararshi Anwar yayi sei yace falalar qiyamullayl..... Faisal yayi ajiyar zuciya yace toh seika pada MA Wanda beiyi 😅

Har zasu pita Faisal yace Kai Ina babbar rigar ka😏.... Anwar yace bazansa ba seikace wani tsoho.... Faisal ya ce toh ni NE tsoho knn.... Batareda Anwar yabashi wata amsar ba... Ya nufi hanyar mota.... Faisal yabishi Abaya.... Suka shige cikin. Wata shegiyar Benz hadaddiya 😍😘..... Sei hanyar ibzy Britain college.... Seida suka kusa makarantar sannan yatuna ashe beigaida mum ba ya dauki waya yakira ta suka gaisa sannan yafada mata beigida Yana skool tace toh Kuma tashi masa albarka.

💐ZABINA 💐 22&23
Horn take.... Maigadin yayi sauri ya Bude Gate... Wata qatuwar gidan hadaddiyar gida Mei kyaw suka sauka suka... Shiga parlour wajen anty kareema

Inawuni anty kareema..... Yawwa yakuke yanmata cike da faraha matar baffansu ke masu magana..... Tare da umma kuka zo.? A'a suka amsa atare.... Ina zuwa haka duk kun sha ado... Dariya kawai sukayi amra tace makaranta muna wani event ne.. Ok toh yayi.... Ta Kira yar aikinta saadarh(dabai 😂).... Dasauri taxo ganinan hajiya.... Kidauko mun soft drinks a fridge kibasu amra...
Takawo musu malt Mei sanyi suka sha...... Uncle Abdulrasheed Baya nanne ameera ke tambayar anti kareema wacce take Zaune duk tagaji alaman juna biu ne da ita..... Eh yayi tafiya tafadi a hankali..... OK toh...... Bari muzo mu gudu Kar muyi latti amrat ta fadi dama ta gaji dazaman...... Tun yanxu 😳kodan uncle dinnaku Baya nanne.... Atare suke fadin a'a amrat tace ai zamu dawo..... Anty kareema tace toh sei kundawo ...suka tashi zasu fita anty kareema Tatashi zata rakasu suka ce tayi zamanta suka fita sei mota wannan Karon amrat ce tayi driving .

Su Anwar ko har sunkai makaranta sei zazzare ido yake kamar Wanda ya Bata hanya... Shidai amrat yake nema yaduba ko Ina beiji taba seiyaji bei jidadi ba...... Mood dinshi ya canza Faisal ya lura da hakan Amma sei bei masa magana ba.

Su amrat suka yi parking cikin skul.... Ameera ce tafara sauka.. Ganin Anwar daga nasa yasa taji wani kalar dadi a zuciyar ta ji tayi kamar tasa gudu tayi hugging dinshi

Amrat tasauka ahankali... Ta rufe motar ,tafiya suke cikin izza da taqama tamkar amaare barin MA anty amrat wacce ta cincibi kwalliya afuska.... Masha Allah ga qamshin turaruka na Taashi kowa Yazo kusa da su sei ya sake kallon su..... Su Anwar na Zaune Kan kujera ta wajen cafterian abokanansa nata labari shidai shuru yayi Yana ta kallon su.... Faisal ya rasa gaane masa Amma da alamar akwai abunda yake nema..... Su amrat sukazo zasu shiga cafterian Anwar naganinta(amrat) yaji wani dadi beisan lokacin da yasaki wani murmushi ba.. Ameera ko kamar tana jira tayi masa murmushi dukda shi ba ta ameeran yake ba seidei yayi qoqarin mata dariya.. Sei kallon amrat yake wacce take taku Dai da kamar tana tsoron kasa take.... Faisal daya Dade Yana kallon abokinsa Wanda ya shagala da kallon amrat yayi murmushi a zuciyarshi yace dama ita Anwar ke ta nema yayi ajiyar zuciya yace seems my freind is in luv😊

Itakam Bata lura dashi ba tashige cafterian abunta..... Tazauna tare da su deeylerh Aa Rasheed dasu ramlat suna ta hira abunsu hankali kwance.....
Anwar ya tashi ya shiga library... Amrat ta hango shi ta window tayi sauri ta tashi tace masu deeylerh gatanan zuwa....

Tashiga library ahankali taganshi yaxauna da littafi ahannu Yana dubawa.... Ahankali take tafiya har ta isa wajen shi sei Kuma takasa Cemasa komi... Harta juya zata fita seiyace mata where to? Ba Shiri haka da juya ya nuna mata kujera tazauna..... Kusa dashi qamshin turarenta nata masa dadi (beisan turaren aro bane na anty ameera ne Wanda tasa ayo mata sabida Anwar)...... Shuru sukayi bamei MA wani magana alamar kunyan juna suke ji......  Amrat ce tagaji tace Mei sunan littafin Nan ya dago littafin nuna mata Bayan taga Sunan "THE GOD'S ARE HUNGRY" nanfa suka shiga labari.

💐ZABINA 💐 26&27 na miminnoor

Ahankali ya dauki dankwalin ta yasaka mata am sorry ya rada mata akunne sannan yadauki wayanshi yafita...... Zama tayi Kan kujera jikin ta duk yayi sanyi..... Ameera tashigo "ke dama kina Nan.... Wancan ba Anwar bane Naga yabar Klass din ynxu ba... Duk amra tabita tsargu tashiga kame kame..... Ameera ta lura da hakan" wae ke menene ko Yazo yafada Miki wata maganar ne Kuma " dasauri amrat tace no bakomi kawai shigowa yayi ya fita

Toh seiki Shirya mutafi baba japaru na jiran mu..... Uhm kawai amrat tace jiki asanyaye Tata shi... Sannan ameera ta lura da shirt din jikinta...

Wannan Kuma shirt din waye kikasa... Ajiyar zuciya amrat tayi tace Ina ruwan ki ne kedai mutafi. Dariya ameera tayi hade da cewa toh muje. Suna shiga mota amrat ta hade Kai da gwiwa... Harsuka Kai gida shuru tayi.

I Anwar Kuma fitan dayayi bei nufi ko Ina ba sei mota ya yi startn mota knn Faisal ya Bude kofar motan.... Oh Wai tafiya zakayi kabarni. Sei kace nayi laifi... Anwar bei ce komi ba yaja mota suka fita...... Driving yake Amma kwata kwata ba a hayyacinsa yake ba jikinsa rawa yake har mota nanemar kufce masa........ Salaati faisal yashiga yi Ganin yanayin da Anwar yashiga.

Parking yayi Yana kokarin maida numpashi........ Meyasameka Anwar kafada mun hankalin Faisal duk ya tashi, dasauri ya fita a motar ya koma driving seat, Anwar Kuma yakoma dayan

Gidan su Anwar Faisal yanupa, cikin Yan qanqanun lokuta suka Kai... Dakin Anwar sukayi direct Kan gado Anwar yafada, .... Gabadaya idanun shi sukayi jaaa

Anwar r u okay ? Yes bakomi Anwar yafadi ahankali..... Faisal yatsaya Yana kallon shi.. katabbata? ... Murmushin Dole Anwar yayi yace yeah u can leave...... Tashi Faisal yayi yafita yarufe masa kofan daki.

Yana fita Anwar yajayo pillow ya rungume sosai.... Yana magana shi kadai "y ds feelings, y? Haka ya kwanta har bacci yayi awun gaba dashi......

****
Bangaren amrat ko tana shiga gida ta gaida su mum sei dakinta.... Bayi tashiga tawatsa ruwa tayi alwala tayi sallah

Bayan ta idar ta Haye gadon ta, rufe ido tayi dukkan abunda yafaru yake dawo mata, abun da Bata taba yiba, sei Kuma tatsinci kanta tana murmushi Kuma tarasa dalili..... Ahaka tayi bacci ko abinci Bata nema ba.

*Bangaren ameera*
Bangaren ameera kuwa Bayan tafito wanka tayi sallah tanupi dinning taci abinci..... Komawa daki tayi ta dauko wayarta tana kallon hoton Anwar Wanda tamai batare da saninshi ba lokacin Yana magana da Faisal... Kallon hoton take tana murmushi tana shapa pix din..... I love you Anwar tafada ahankali tareda peckn hoton..... Deidei lokacin call din Yayanta yashigo, murtuqe fuska tayi tadanna reject saanan tasaka wayar a airplane mode tacigaba da kallon pics din Anwar, Akan qirjinta ta kife wayar da hoton ahaka Itama tayi bacci.

Kuyi haquri 🙏🏻nagaji insha Allah Nan da anjima zaa qara
Taku miminnoor.

💐ZABINA 💐  28&29 na miminnoor

*****
Tunda asuba yatashi yayi wanka yayi alwala yatafi masalaci. Bayan an idar yadawo Dakin shi ya kunna waya..... Whatsapp yashiga yafara chatting as usual..... Yashiga contacts yafara dubawa Cas yaci karo dasunan shi Anwar (amrat)... Murmushi yayi yayi viewing din display pix dinta hoton ta ne da ameera... Ba tareda Bata lokaci ba yayi saving sannan ya shiga gallery yayi croping dinta😬yacire ameera......... Lucky 4 him komawa WhatsApp din da zeiyi she was online Amma yarasa yanda zei mata magana

Dakyar ya yi typn hy angel don da dayayi typn sei yayi deletn...

Message din takaranta...... Ganin sunanta ne yasa tayi saurin gaane kowaye.. Amma Kuma Jan aji namata yahanata amsa wa

Can yaqara mata magana sannan ta amsa da sallama... Nanko suka fara chatting tun Bayan sallar asuba sei 11:00am suka sauka..... Hakan Yama Anwar dadi har ya bashi qarfin gwiwan Kiranta a waya...... Kullum na kullu yawmin basu da aiki sei chatn da call dukda wasu lokacin amrat takan ja masa klass

Kamar wasa hutu ya kusa qarewa.... Danko har anyi sati biu da hutu.... Abu Kuma ya qara qanqama tsakanin amrat da Anwar... Har ya iya askn dinta out... 🙉...... But taqi bashi reply Wai she wants to think about it😒

Amma Kuma a haka take bayyana masa kishin ta.... Badaman yasa hoton mace ta dinga bala'i knn Kuma tahanashi sa nata.... Pic din amrat awayanshi zan iya Cewa ita tayi making gallery dinshi dukda Cewan da kyar yasamu

*****ameera ko tunda akayi hutu Bata da aiki banda kallon hoton Anwar ta rasa inda zatayi tasamu numbern shi..... Kullum tana daki kamar marainiya sei akin rungume rungume, har anrasa Gane mata a gida......

Kuma wacce zata iya debe mata kewa itace amrat seidei ita amrat x always busy with ha fone,aduk lokacin da ameera ta shiga Dakin amrat sei ta sameta ta na call, safe Rana yamma dare 😓Kuma abunda yafi daurewa ameera Kai shine aduk lokacin da tasameta tana waya amrat naganin ta sei ta katse wayan kamar marar gaskiya.... Tun tana boye abun yanxu har tadaina seidei ameera batasan dawa take yawan waya ba

***
Shima Faisal ya lura Anwar bashi da lokacin shi yanxu.... Kullum seidei ya dinga waya da wata

****
A last 2 weeks of the vacation Anwar yashiga rashin lfya kullum shine ciwon Mara Kuma yaki fada Wa kowa banda Faisal

Ciwon mara😳Kai miya hadaka da ciwon Mara Kuma.... Lallei baba akwai aiki agabanka

Cikeda rashin ganewa yake tambayar shi kamanya Kuma work.... Nifa nazo ne karakani asibiti

Dariya Faisal yakeyi harda riqe ciki.... Yooo Kai ynxu waya fada maka seikaje wani asibiti ai Bata lokaci ne kawai

😏Anwar yace Bata lokaci Kuma zaka bani magani ne... Murmushi Faisal yayi sannan yaafara masa explanation 😉nidei banji ba don ahankali yake masa, seida naji Anwar yace sha'awa Kuma? Kana hauka

Faisal ya tabe baki yace matsala na dakai Kenan, kacika Abu kaman Saint

Hum tere he kasam Hum savar jaayenge 🎤🎼........... Murmushi tasaka don tasan Wanda ke Kiran ta, tayi sauri tasauko daga stairs sei dei wayan na hannun ameera Kuma hartayi pickn.... Ke amrat ta Kira ki..... Uhm kawai amrat tace ta amshi wayan ahannun ta

Ta shiga dakinta tasa mukulli ta rufe.... Dire wa tayi kangado ta kunna data sei chattn..... Bayan Yan mintuna Anwar yakira ta.... Tana dauka suka gaisa.... Cikin tattausar murya tace sorry dazu ka Kira bana kusa da fone... Seida yayi ajiyar zuciya sannan ya ce bakomi dama Naga andauka sei Kuma naji ba voice dinki bane

Budan bakinta eyyeh har kasan voice dina.... Dariya kawai yayi hade da cewa sosai ko

Kinsan a voice dinma naki dabanne so sweet.... Words can't explain.... Itako sei dariya take

Ya naji yau muryar ka so low ko bacci kakeyi ne

No dearie Bana Jin dadin jiki na ne Mara na naciwo

Cike da damuwa take masa tambaya... Toh meya kawo hakan? kaje asibiti? kasha magani? ya kakeji? kafada wa mum? Kaci abinci? hope dei it's not critical?

🙄amrat take it easy.... Wanne zan amsa? AM okay dear... Faisal ya ce I need not to go to the hospital Wai dakanshi zei barni...

Ahankali tace I hope so..... Tambayanta yayi cikin wani cool voice amra can I ask u a question? Tace of course yes..... Errrrr r u still thinking about it? Kinsan yanxu it's been almost 3 weeks ynxu uptil now banji reply ba 😔

Shuru tayi ba magana sannan ta ce em I've tot abt it ND nayi accepting on 1 condition.. U will let d relationship between us be a secret

Anwar yace y? Meyasa kikeso yazama secret

Shhhhh no questioning.... Bayanda Anwar ya iya yace ohk agreed...... Tace promise yace deal......ahaka suka qare wayar

Ceiling Amrat tashiga kallo tana murmushi alamar tashiga wani planet na tunani

Shikuma a bangaren shi tsalle yake Akan gado Yana ihuhu yes yes at long last.....

💐ZABINA💐30&31 na miminnoor

Shirye shiryen komawa makaranta suka fara yi..... Ameera tafi kowa dauki sabida zata ga Anwar...... Yanxu saura Sati daya suko MA skul

*****Anwar duk yabi ya matsu yaga amrat dinshi..... Daga waya yayi yakira ta...... Sei da ya kusa katsewa sannan tadaga

Hello kuchee na wulaqanci zakimin ko.....

Aa me kagani.... Dariya Anwar yayi yace bakomi nazaci bazaki daga wayar bane

Kai ni na Isa naki daga wayar habibi na......

Yayi wani qasa da muryar shi yana mata shagwaba... Wllhy baby Ina missing dinki can't wait to cee u........ Ko nazo gidanku ne?

Gdan mu😳hmmm aa dei bansan Mei zanfada masu umma na ba

Hmmm toh yanxu ya zanyi nifa inaso naganki

Ai zaka ganni ranar Monday....... Ajiyar zuciya yayi kawai.... Nidei inaso kafun Monday

Toh kabari gobe zanje gidan anti kareema sei mu hadu a can.... Cikeda farin ciki Anwar ke magana Ina ne gidan....... Dariya tayi tace zanturo maka address din....... Dadi Anwar yaji Mara misaltuwa zeiga amran shi

Next day........                      Da yamma amrat tayi  wanka, tasaka yar jallabiyar ta Baki da pink shoe da pink small veil dinta,tarataya jakar zamaninta pink ta feshe jikinta da turaruka masu kamshi...tayi Dan simple make up din ta tayi kyaw sosai.....

                                       Saukowa tayi Daga dakinta semi tayi dakin umminta ,nan suka ci karo da ameera....

Ko INA zuwa kinci kwalliya haka,ameera na tambayar amrat wacce ke kokarin bude dakin ummi....

                
  Gidan anti kareema,INA kewarta ne. Oh shineko kifadamun,seimu tafi tare haba swt sis****          

murmushi amrat tayi tace,kedei bari,yanxu ai its not too late zan iya jiranki kishirya,sei mu taxi*******                  

yawwah amratutun umma ,bari nayi sauri nayi changing, dasauri ta haye sama tashiga dakinta,ta canza kaya,itama jallabiya tasaka,da veil din abayan sannan tasaka takalmi peach da jaka peach.we Dan powder da wet lips.ta peshe jikinta da perfumes**     

saukowanta keda wuya ,semi ta jiyo sallamar yaya Sadiq wani dadi taji aranta danko ba kadan tayi missing yayanta ba,seidei kuma semi taji wani haushi Kawai Dan yanxu ita anwar takeso***********           

ita bawai batason yayanta bane Kawai de qawnar anwar ya rinjayi na yayanta ne**   

ahankali ta sauko. tana had a ido dashi,tawani kwakwalo murmushi ,shima murmushin yamata yace,INA zuwa haka kinyi wani kyaw kamar balarabiya *********** 

   sa hannu tayi tarufe fuska alamar kunya,tace yaya sadeeq wannan dei zolayata kake.......

Sadeeq yace aa darlin ba maganar wasa ba dadin wannan kawai mufita yaawon mu ko sweedy

Murmushi meera tayi tace zamu gidan anty reema ne fa nida amrat

Matsowa yayi kusa da ita ya Na kallon cikin idanunta tayi sauri tasa hannu ta rufe fuskar ta 

Cire hannun yayi yariqe sannan yafara mata wasu maganganu
*****
Meera na nakosa naganki a dakina zanso kizamo uwar kids dina kece jigon rayuwa ta shuru tayi tana kallonsa.... Yacigaba Amma Naga kwanannan wulaqanci kike munne ko kinada wani ne meera kifadamu fadamun

Wata yar guntun hawaaye ne ya zubo mata don ko tana feeling guilty... Gani take tana yaudarar Dan uwanta itafa ynxu Anwar takeso

Meera Meye Kuma na kuka duk hankalin shi yabi yatashi qoqarin share mata hawaaye yake ta wani rungame shi tana Yaya na ba wulaqanci nake maka ba

Suna hakan ne amrat tashigo gyara murya tayi da qarfi.... Dasauri suka Saka juna

Toh love birds sannun baku tsoron umma tafito ko... Meera sunkuya Kai tayi don sistern ta Bata taba Ganin ta tayi hug da wani ba

Shiko gogan ko ajikin shi... Tsokanar amrat MA yashiga yi kamar yanda yasaba sannan yace little zaki ban Aron mata ta zamu fita yawo......

OK gidan anti reema Kuma tapasa zuwa knn.... Toh nabaka aronta Amma ba kyawta ba

Dariya sadeeq yayi yace toh Godiya Nike Bari na gaida Abba nadawo

Amrat tazaro ido tace dama baka gaida abban ba

Yafara Sosa Kai Yana ai dama nace Bari nafara Ganin wifeey na ne nasamu nutsuwa

Toh angon ameera Nina barku bye

Ameera dei zuba masu ido tayi Dan tasaba da dramar su

Cikin Yan mintuna amrat takai gidan anti reema.... Fortunately uncle Abdulrasheed Baya nan..... Anty reemah taji dadin ganinta har tana tambaya Ina ameera

Labari suke amrat take Bata labarin Anwar Kuma tafada mata zei zo..... Anty reema taji dadi sosai har tana tsokanarta da Sunan shi

Wayanta yafara ringing tadauka..... Tace ok ganinan zuwa ko zaka sauko ka gaida anty na.... Bamusu yace toh danko Anwar ashirye yake yayi meetin kowa Koda dad ne.

💐 ZABINA 💐31 & 32 na miminnoor

Yashigo da sallama, suka amsa masa, durka wa yayi ya gaida anty reema, da faraha ta amsa tace yaxauna mana

Girgiza kai anwar yayi yace a'a Anty basai na zauna ba,dariya anti reema tayi tace ko kunya na kakeji?

Anwar yace a'a,tace to shikenan,yace to Anty bari Muje waje,tace a'a Barin bar muku nan koya kikagani amrat amrat idonta akasa taki amsawa se anwar yace a'a baride muje sei tace to shikenan se ya fice amrat ma ta bishi a baya mota suka nupa direct.....

Nanfa suka shiga hira..amrat ta CE yajikin naka mahboub yace alhamdulillah my precious angel.nayi missing dinki lyk hell,dariya tayi tace yazan yarda da hakan

Haba baki gana rame ba dariya tashiga yi masa tana ai bani NASA ka rame ba

Kece mana kin hana ni ganin ki

Ni Kuma a'a Kar kamun sharri baruwana, ni nama fisonka ahaka yanda karaame... Kaga zanfi samun chance din maka dariya danko yanxu nafika qiba

Zaro ido yayi yace habba dei *kucchi na* idan kika fini qiba akwai matsala, kefa banda hips da kuma boo....🙊seiya Kuma yayi shuru

Toh ka karasa mana
A'a bazan qarasa ba

Aiko tafara surutu
Ai Sei ka qarasa... Ko ka qarasa ko muyi ta ynxu ko.... U beta say wats on ur mind or else sei yi take taki shuru

Shiko zuba mata ido yayi... Daya gaji da surutanta ya daura hannu Akan lips dinta

Shhhhh!!! Kinfiye tsiwa da surutu Kuma nasan maganinki..... M kallon shi kawai take yanda taga yayi serious

Bakinsa yakai kannata yafara tsotse mata lips... Tunba tada niyyar tafara kissing dinshi Itama

Tsotse lips Din junna suke... Ahankali ta zame lips dinta ya qara janyo ta...... Zei cigaba tace mahboub ya isa pls.... Bei ishe niba yarada mata akunne kitaimaka mun pls wllhy Ina needn dinki ynxu tunda akayi hutu bansamu nutsuwa ba kawai karfin haline idanun shi sukayi jaa harda Dan hawaaye

Batace komi ba ya kama lips Din yacigaba da kissing dinta ta riqe masa hannu tsoron Kar yakai hannun shi wani waje ajikinta

Shiko sei murza hannun yake Yana yi Yana hura mata iska a kunne

Lumshe ido takeyi kamar tana Jin bacci

Rungume ta Anwar yayi Yana qoqarin maida numpashi, zufa yayi sosai, qara matseta yayi ajikin shi ...... 4 d past 2 weeks marar shi acike take sei yanxu yasamu yayi releasn

Tausayin shi amrat taji sabida tasan harda qamshin turarenta(Wanda ameera tasa akayo mata sabida Anwar) Yana cikin abunda yatada masa sha'awa.

*Bangaren* *su* *sadeeq*
**********

Bayan sadeeq ya gaisa da Abba sannan yatafi bangaren umman ameera yagaisheta Kuma ya nemi izini zasu fita da ameera tace adawo lfya

Hanyar Disney chicken sukayi.... Suna kaiwa yayi parking yayi sauri ya je ya Bude mata qofar ya karbi jakan hannunta

Zaro ido tayi tace honey Mei Kuma na qarban jaka anafa kallo

Toh ke meera na Ina ruwanmu da mutane...... Ai ynxu MA zan iya daga ki dan karki wahala.... Dariya tayi tace no habba dei.

Riqe mata hannu yayi suka shiga Zaunar da ita yayi yamiqa mata jakar ta sannan yaje yayi ordern

Bayan ya dawo ne call yashigo masa tashi yayi yabar wajen yayi recievn.

Kafun yadawo.... Faisal yashiga wajen ya hango ameera azaune.... Ahankali ya taka wajen ta

Sallama yayi mata tana dago Kai taga ne shi amsa sallama tayi tace abokin Anwar ko

Yace eh Faisal sunana.... Dama Ganin ki nayi nace Bari mu gaisa

Allah sarki toh nagode har zei tafi tace pls zan iya samun numbern ka da na Anwar... Yace sure bt y do u need anwars number.

Nothing jst for zumunci... Faisal yace alryt ya Bata numbernko fitan shi keda wuya sadeeq yadawo

Sorry princess na Dade ko.... Dariya tayi tace not at all...

Gabadaya fuskar ta yacanza har wani qiba tayi sei murmushi take

Sadeeq ya lura da hakan... Princess Naga kin wani yi kyaw ne ynxu nnan dariya kawai tayi.

Sannan aka kawo musu fried da chicken 🍗 da chi exotic....... Best drink din ameera.

💐ZABINA 💐 33&34 na miminnoor

Bayan sunci suka tashi zasu tafi, ya sayi ice cream guda biu da shawarma guda uku Wai biu na meeran shi daya na amrat (😂 kaji sankai)

Har gida ya kaita ya sauke ta... Hakan yayi dei dei da isowar amrat da Anwar

Sadeeq yashiga da mota shi Kuma Anwar yayi parking a kofar gida

Sundan Dade suna lbry da amrat sannan ta ce mahboub Bari na shiga gida.....it's getting late ynxu Yaya sadeeq zei fito
Sukayi sallama Anwar yace take care of ur self 4 me kucchi na

Tanako sauka tana qoqarin rufe motar Yaya sadeeq din yafito

Ahankali  take tafiya har ta kai gate din ta gaida shi... Sei yanxu kuka dawo take tambayar shi

Gyada mata Kai yayi alamar eh..... Waye Kuma wannan ya sauke ki a qofar gida

Errrr soshe soshe tashiga yi ai skul mate dina ne...... Ko Kuma saurayin Kiba sadeeq ya fadi tun kafun amrat ta kara magana

Batace komi ba tace Yaya barina shiga ciki.... Toh sei dasaafe little din Anwar

Zaro ido tayi ta yi sauri ta juyo... Kallonsa take cikeda da mamaki a fuskar ta Yaya kasan mahboub ne oh sorry Anwar

Dariya sadeeq yayi yace har wani mahboub ake kiranshi lallei ne toh nasanshi sosai

Abokin Kane shi... Sadeeq yace a little he's a family freind ... Gaayen bayi da matsala

Murmushi tayi tace eh Yaya wllhy bayi da matsala.... Sadeeq yace eh. Little angirma har ansan luv..a zuciyar ta tace har abunda yafi love nasani Dariya kawai tayi tace sei da safe yaya

Tana shiga gida kuwa taje ta gaida su umma.... Ko abinci Bata nema ba danko taci ta qoshi agida anty reemah

Dakin ameera ta nupa direct tanazuwa tafada Kan gado ta

Ameera shawarma take takewa da ice cream..... Ganin ice cream amrat tafara biyyaya

Anti meera ya outing din

😳yau Kuma nice anty lallei NE ma Kodan Kinga ice cream 😂toh idon ki ne yagani Amma bakinki bazei taba ba

Habba mana anty meera pls yahakuri daga yau zan dinga Miki biyyaya

Dariya Meera tafara yi... Kin tabbata

Amrat tace Eh mana....

Toh dauki naki dama daya nawa daya nakine

😬seida ta cinye shawarman tashan ye ice cream din tafara surutu

Yawwa meera ya outing dinnnaku.... Ban lbry

Ajiyar zuciya meera tayi tace Ina kika ijiye antyn

Ok toh anty meera pls gst me

OK sis... Nthn much kawai Disney chicken mukaje munyi fried rice ND chicken sei mukayi labari... Yayi planning future dats all

🤔amrat tace u mean dats all... Sei kace kinfita da abokin gabanki nthn romantic

😱Kai amrat r u crazy wat do u mean... Dan Allah amrat don't judge me wit wat u saw dazun wllhy its nt wat u think, pls sis karkifada MA kowa nasan halinki... Ynxu zanmiki wani laifi kifara threatening dina kice zaki fada wa umma na

Dariya amrat keyi harda qwarewa

Ameera ko tarasa meke Sata dariya..... Bae wats funny. Y r u lafin

Hmm nthn oo.... But wats Dia Dan kunyi hugging Yaya sadeeq it's a normal stuff ai

Cikeda mamaki ameera ke Tambaya... I dnt get u... Wait don't tell me u've been on ds kinda stuff already

Rufe fuska tayi Wai ita kunya 🙈tace sum hw

Aw habba tell me swt sis wu x d lucky guy ameera taqosa taji kowaye

Dariya kawai tayi tace my mahboub.... Yafi Yaya sadeeq kyaw fa... Meera if u cee him... Hmmm

Meera tace really... Hmm lallei NE shine ko ki fada mun.... Banji dadi ba gskya bt sha m happy 4 u Allah ya barku tare

Ameen meeran sadeeq

Azuciyar ameera tace meeran Anwar dei

Tashi amrat tayi ta nupi dakinta bayi tashiga tawatsa ruwa tayi alwala tayi sallah Bayan Nan tayi addua Allah ya mallaka mata Anwar

Tanagamawa ta dire Kan gado agajiye tadaga wayanta ta Kira anwar

Hello mahboub dina kakai gida lfya?

Yace eh kuccheee na kiyi haquri bnkira ba... Dad ne yakira ni muna wani magana dashi ne

Eyyah hope dei ba matsala mahboub

Ajiyar zuciya yayi yace eh toh.... Idan muka koma skul I will tell u

No mahboub no ynxu nikeso kafada min.... Tafara masa shagwaba

Duk tabi ta kashe masa jiki don ba kadan ba Anwar na son shagwabar kuccheeen sa

Aa sweedy dadei kinyi haquri mukoma makaranta wannan ba maganar waya bane

Ohk honey na haqura... Allah ya kaimu.. Ameen ya amsa mata

Toh ynxu dei kije ki yi bacci banaso kiyi stressing kanki

Uhm tace gud nyt habibi yace gud nyt habibati

Harzata katse yace baki mun peck ba 💋 ahankali tace umuah 💋💋

Enx luv gud nyt Itama tace nyt.

💐ZABINA 💐 35&36 na miminnoor

Dasaafe qarfe 10:30am ameera ta dauki waya ta Kira number Anwar.

Hello salama alaykum Ina kwana

Waalaykumusalam wake magana pls

Cikin tattausar murya tace Sunana habiba u Lawal Kuma am ur skul mate mate

Oh really wani class kike

Tace mune ss2 na yanxu inshallah

Eyyah dats gud bt pls Ina kika samu number na

Murmushi tadanyi ta ce frm ur frnd Faisal

Ohk oo he's a trusted partner

Tace take care yace olryt

Anwar da ameera suna chatting... Seidei bei taba Cewa taturo masa pic dinta ba

Don haka beitaba Ganin fuskar taba
Seidei yace idan ankoma skul zasu hadu

******
*Monday* *morning*

Ankoma skul.... Dadi awajen ameera Baya misaltuwa danko ita harta hango nasara

Tsap Tsap tashirya tayi parking gashinta da black ribbon tasaka vest black da tight black duk sun fito danko bata rufe upper button din rigar ta ba

Anwar ko ya qosa ayi break yaga kuccheeen sa......

Lokacin break yayi... Amrat tana class Bata Gama note ba

Ameera tafita tayi upstairs ta ci karo da Faisal su ka gaisa take tambayar sa Ina Anwar

Hakan yayi dei dei da tahowar Anwar.
Murmushi tasaka masa

Faisal yace gashi Nan MA Bari na barku ko

Dasauri tace kagaane ni

Anwar yace no banganeki ba

Seitace habiba u Lawal ce

Yace oook haka fa nace zamu hadu a skul yau ko yakike

Tace lfya

Anwar yace u r cute

Ameera baki har kunne tace thanks bt ai kafini

Nan sukayi lbry..... Suka Gama tayi hanyar cafterian shi yasauka.... Yana sauka amrat na Hawa stairs

Kicimus sukayi tace mahboub Ina zuwa

Anwar yace dabanganki ba ne nace Bari na dubo ki

Dariya tayi tace note ne bangama ba

Oh baby Dakin bani na tayaki

No banison nawahalar dakai

Murmushi kawai yayi suka shiga skul hall bakowa... Can end of hall suka je suka zauna

Suka sha tadin su.... Riqe mata hannu yayi Yana murzawa Yana Bata flows masu kashe jiki 😜

Ameera nacan cafterian tana Tunanin Anwar... Qoqarin Hada plan take Akan yanda zata sace zuciyar Anwar

Amrat ta tuna yace zei fada mata wani Abu

Mahboub kace zaka fada mun abunda dad yafada maka

Oh kucchi namanta

Ohk ynxu natuna maka sei kafada mun

Yadan sunkuyar da Kai baby its not dat good news

Hankalinta atashe
... Menene kafadamun pls
..... Menene

Dama dad yace bazan qarasa karatuna anan bane... Kinsan ynxu tunda Ina ss3 Bana Tunanin zan Kai wannan term din

Toh pha mahboub.... Ina zakaje knn

Yace nazaba btwn dubai da Istanbul

😔ynxu mahboub shknn zaka tafi kabarni all alone ko

Hada hannun ta yayi yariqe sosai Yana sauke numpashi..... Ai bazan Dade ba 3 yrs ne kawai.. Kinsan civil engineering Baya daukan much tym

Toh Allah yasa mudaace

Yace ameen kuccheee na... Yayi peckn hannunta

Har aka tashe su makaranta amrat batajin dadi don harta fara missn mahboub dinta

Tanakaiwa gida tayi usuals dinta ta haaye gado tafara tunanin yanda zatay

Kawai wata dibara tafado mata..... Tashi tayi dasauri kamar ankira ta daga ita dei yar short gown da Bata Kai gwiwa ba dakadan ya wuce duwawunta 🙊

Dakin umman ameera tashiga dasauri ko sallama batayi ba

Ke sophiyya miye haka kinwani Fado mun daki ko sallama bbu

Sorry momma dama wani abune na gani a wata magazine nace namiki sharing

Toh Ina magazine din

🤔ai Yana skul

Umma tace Ina jinki

Amrat tafara wasu skuls ne nagani University dubai da kuma na Istanbul.. Em shine suka mun nace Bari na fada Miki

Umma tace ynxu miye naki da tunanin University ynxu... Kuma meyasa ba zakiyi studying a Nigeria ba

Data rasa abunda zatace seikace Yaya
abubakar yasan da maganar...... Kuma yace makarantun suna da kyaw especially 4 me tunda medicine zan karanta, umma can 4 yrs ne nankuma 7yrs... Umma bakiga difference ba

Tafadi wa  umman ameera ne sabida tasan umminta bazata saurare taba Kuma tasan umma tanajin kunyar Yaya abbkr shiyasa tayi qarya da sunanshi

Ajiyar zuciya umma tayi tace I will speak with ur dad u can go
Tsalle tayi ta yi hugging umma... Thanks umma u r d best...

Harta Kai kofar dakin sei tadawo tadauki 2k a gadon tace thank u kamar anbata... Sannan tafita.

Dariya umma tayi tace Allah karaya mini su

Ameera nadaki suna chatting da Anwar tagani a status dinshi..... Dubai on my mind already missn kucchi

... Wani kalan zazzabi ne ya lulu beta har Bata lura da already missn kucchi ba

Tayi sauri ta tambaye shi zei tafiya ne

Yace eh... Yabata lbryn zeije studying a dubai..

Yawo tafara yi a daki don gabaki daya plans dinta sun rushe

Daga waya tayi ta Kira rahma... Tafada mata komi

Tsaki rahma tayi tace shine kika wani rude haka.... Kibashi mana ai ubanki nada kudin

Bata Bari rahma ta karasa ba takashe wayar tana dariyar nasara

Toh ya zatayi convincn abban su.

💐ZABINA 💐 37&38

Waya ameera ta daga takira uncle rasheed ta masa bayani da dadin baki
Yace toh zei MA Abba magana....

Ameera tajii dadi sosai

****
Da dadare amrat da Anwar suna waya yake cemata ya zabi dubai Kuma in a months time zei tafi

Amrat harda Dan guntun hawaayenta don tasan Koda zataje studying a dubai din ba maganar ynxu bane sei tagama ss2

Babban abun dake sata fargaba... Kada yaje can yamanta ta
Tace toh mahboub zansa ka a prayers Allah yasa mudace

Yace kuccheeen Anwar yanaga voice dinki na shaking kona Bata Miki raine
Tace not at all kawai na fara missn dinka habibi na

Yace nafi missn dinki

Haka suka qaare waya

Lokaci nata tafiya... Amrat da Anwar suna qara Shakuwa... Ameera kuwa harsun saba da Anwar... Seidei harynxu shi Anwar beisan ameera yar uwar amrat bace duk da amrat takan bashi lbryn ta seidei beisan ta da ameera ba seidei habiba

Haka zalika ameera batasan Anwar ne saurayin amrat ba dukda amrat takan Ba Ameera lbryn shi seidei da mahboub take kiranshi

*after* *a* *month*
*****
Ranar Friday lokacin break Anwar yakira amrat suka hadu a library... Yake fada mata ranar Sunday zai tafi

Sukayi magana sosai

Yace kucheena kimin alqawarin bazaki barni ba

Tace mahboub I promise u bazan Barka ba kaima kamun alqawarin bazaka yaudare niba

Yace namiki alqawarin haka

Kucheena idan nagama karatu sei nafito ko.. Jst keep ur self for me burina kizamo uwar kids dina... Yarike mata hannayenta sosai ya azakai a hannayenta seiji tayi hawaaye Akan hannunta

Mahboub badei hawaaye kake bako

Yace badole ba Ina tsoron rasaki

Murmushi tayi tace insha allahu bazaka rasani ba

****
Ranar Sunday  dasaafe Anwar ya Kira amrat yace Yana airport sukayi bankwana....

Ameera kuwa tana Nan batasani ba... Seida Faisal ke fada mata

Wani sanyi NE ya lulu beta.. Ynxu shknn tadena Ganin amrat dinta... How she wishes Yana sonta inama ace yasan tanason shi yazatayi taganar dashi... Ganin batasamu amsar tambayoyin ba yasa tafashe da kuka.... Kuka take sosai Mei tsuma rai

Bayan sallar Isha Anwar yakira amrat yace mata ya isa.... But yagaji zasuyi magana gobe

Bagardama ta ce seida saafe

Ijiye wayan shi keda wuya ameera takira shi.... Yadaga

Tace kana inane..

Yace sorry habiba namanta nafada Miki ynxu Ina skul middle sex University dubai

Allah sarki ya journey Anwar yace alhmdulilah

Tace ynxu Dai kagaji u need to rest... Take care dear

Anwar yayi mamakin haka Amma bei dauka da wani ma'ana ba yace thanks

Dassasafe sms yatashe shi yanadaga wayar yaga habiba ce yabude ya ga mrnin sms "d sun x shining d sky x bright d birds r singing and I am saying  to ds gentle soul...GUD MRNIN

murmushi kawai yayi bei mata reply ba ya tura MA amrat dinsa" feeling lonely and blue without you ND wishing u were here by my side gud mrnin my hrt desire

Itama qarar waya dataji yataashe ta... Ganin mahboub ne ya turo mata sms yasa tayi murmushi... Tana karantawa tarugumi wayar ta

Tamasa reply "badly missing yhu my mahboub Allah ya kaare mun Kai

Dadi yaji da adduar data masa.

Tashi yayi yayi wanka yayi Shirya cikin Jan Polo shirt da farar wando 3quater yasa farar socks da farar emax... Yataaaje gashin Kanshi Mei qyalli ya fesa turaruka yadauki jakar shi na goyo yafice daga Dakin..... Dakin babba ne sosai Kuma shi daya ne... Dakin ya hadu iya haduwa

****
Rasheed yayi wa Abba magana Akan makarantar ameera Kuma Abba ya amince... A ss2 ameera zatayi waec... Uncle rasheed ya fadawa meera yanda sukayi da Abba... Dadi awajen ameera Baya misaltuwa dadi takeji sosai

Amrat kuwa... Umman ameera tasa a binciko mata cikin dubai da Istanbul wanne zeifi

Aka binciko mata... Qawar ta umman jos tace Indai medicine ne tayi a Istanbul sunfi karatu... Umma tafada wa Abba.. Yace ummi amrat tasani Kuma ta amince.. Umma tace eh..yace toh shknn itama ss2 tayi waec.

💐ZABINA 💐 39&40 na miminnoor

Makaranta yadaina MA amrat da Ameera dadi

Anwar kuwa Yana ta missn kuccheeen sa arana sei suyi waya sau 10

Itako Ameera seidei ta Kira shi Amma Baya kiranta seidei chat... Ameera tana nuna MA Anwar kawna sosai Amma shi beigaane ba

Sadeeq kuwa Yana makaranta A. B. U abinshi idan yadawo yakan leqo gdansu meera su sha zance

Aduk lokacin da ameera ta ga sadeeq seitaji tana son shi Amma idan ya tafi Tunanin Anwar ke dawo mata

Lokaci nata tafiya..... Kamar wasa lokacin waec yayi.... Sukayi waec alhmdulilah sakamakon yafito sunci sosai Abba yasamu su albarka

Batareda Bata lokaci ba Abba yafara Shirye Shiryen admission dinsu ameera yatura MA ALH BELLO AHMAD takardun ameera

Aka ba Yaron umman jos Dr ammar takardun amrat tunda shi a Istanbul yagama

Abu kaman wasa amrat tasamu admission... Umma takira ta ta fada mata tasamu admission a Istanbul

Ihu amrat tasaka... Umma y Istanbul?

Umma tace ke kika cemun ko dubai ko Istanbul

Kuka dagudu amrat ta hau stairs tashiga daki.. Kuka kawai takeyi ba fullstop...

Umminta ta shiga Dakin ta shiga rarrashinta... Amma Ina taki shuru

Umma ta tambayeta baki son Istanbul ne tagyada mata Kai tana shesheqin kuka

Umma tace dubai kikeso

Tace eh.. Umma tace meyasa

Shuru amrat tayi ba magana

Umma ta rarasheta ta Bata haquri tace taje Istanbul din next year tamata alqawari zaa mata transfer Dan Abba ya Riga da ya biya skul fee

Bayanda zatayi ta haqura Amma bataso ba

Ameera kuwa tasamu nadubai.... Dadi takeji sosai dagudu tashiga Dakin amrat tasamu amrat kwance Akan daduma abun tausayi

Sis nasamu admission din dubai dasauri amrat Tatashi tace habba

Meera tace wllhy next week zanwuce... Amrat tace Nima next week zantafi

Ameera tace Ina? Istanbul amrat tafada ahankali Takoma Kan gado

😞 hawaaye ne masu zaafi suka zubo mata

Hankalin ameera atashe tace wats wrong ain't u happy

Amrat tace Nima nafison dubai

Rungume ta ameera tayi tace it's okay sis zamu MA Dad magana u knw I can sacrifice enytin 4 u

Amrat tace ai dad yariga ya biya Kuma umma tace next year zaayi transferring dina to dubai

Murmushi ameera tayi taja MA amrat kumatu tace ai next year x lyk tomorrow worry not Lil sis

Amrat tace okay

Ameera tace smile.. Amrat tayi murmushin Dole ameera tace bahaka
Ba inaso Naga wushiryar ki pls

Chakulkuli ameera tashiga yi Mata hartayi dariya

*Ranar* *Saturday*
Flight din amrat nasaafe ne... su meera suka rakata airport kuka tayi sosai daga ita har meeran ba mei lallashin wani

Bayan ta tafi
Ameera tashirya ita flight dinta karfe 3 ne

Itama su ummi ne suka kaita...

Ynxu duk sun Kai makaranta... Amrat tana Istanbul ameera Kuma tana dubai

Dakin ameera babba ne sosai Kuma ita kadai ce

Amrat Kuma ita da wata ne a Dakin dayake babban dakine Kuma batason zama ita kadai

Sunan roommate dinta yumna..... Tsawon su daya da amrat Kuma shekarunsu daya... Yumna kyakyawa ce yar Nigeria ce Itama.... Mahaifinta Dan maiduguri ne mahaifiyar ta kuwa yar yola hakan yasa tana Jin fulatanci sosai

Amrat tanajin dadin zama da yumna Kuma ita kadai ce qawarta hasalima department dinsu daya

Ameera kuwa qawaayenta biu da hafsert da sulti

Sulti itace suke nursing department tare da meera wyl hafseee department dinta daban yake

Amrat tayi qoqarin fada wa anwar tana dubai Amma batasamun shi a waya

Ynxu 2 weeks dazuwanzu su amrat skul knn
Umma da ummi suna ta Kewan su

Ranar Friday da Rana kamar qarfe daya ameera ta gwada Kiran Anwar fortunately wayar tashiga

Cikin jindadi take fada masa ai tana dubai Kuma tanaso. Ganinsaa

Bamusu yace su hadu a ALqarnain

Suka hadu.. Anwar yaqara kyaw Sosai hakan yasa yaqara shiga ran ameera

Suka sha coffee
tanata mai wasu kisisina Amma ko ajikin shi don ya Riga ya qudurta bazei saba alqawarin daya MA amrat ba don haka komi tayi seidei yabasar

Amrat kuwa Bata kula kowa har abun Yana ba yumna mamaki

Yumna ta matsu ko ta tambaya amrat meyasa Bata kula samari

Aiko amrat tazayyana mata lbryn ta Dana Anwar har alqawarin data yi masa

Abun ya Burge yumna sosai harta yi musu addua Allah yabarsu taare

Kullum Anwar yakan Kira amrat har video call sukeyi Kai kaace suna taare ne

Hakan Yana ba masoyan kwanciyar hankali

Sadeeq ko yanata kawar meeran shi... Itama tana kewar yayanta.

No comments:

Post a Comment